Skip to main content

Tarihin:- Marigayi Sheikh Muhammad Goni Aisami {Ya Sheikh} Gashua

 GWAGWARMAYAR YADA ADDININ MUSLUNCI DA:

Marigayi Sheikh Muhammad Goni Aisami {Ya Sheikh} Gashua


 A fagen Wa'azi da karantarwar Addinin muslunci akan doron Qur'ani da Sunnah.


 Daga: Shehu A. A. Gashua


    Shashidi sheikh Muhammad Goni Aisami ya farayin fice ne sosai a fagen Wa'azi da kungiyar Izalah take gudanarwa a mako-mako a Cikin unguwanni dake cikin Garin Gashua a shekarar 1992. Shehin malamin ya iya jawo hankalin Matasa da Dattawa a lokacin da yake wa'azi Kuma cikin shikima da Girmamawa.


   Sheikh Goni ya Fara gabatar da Tafsirin Al-Qur'ani Mai Girma a watan Ramadan a Masallacin Juma'ah na kungiyar Jibwis dake unguwar Kofar Halliru Gashua a shekarar 1995 inda Alaramma Idriss Abdurrahman Gashua yake ja Masa Baki.



  Ya sheikh ya Zama shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jibwis na Bade Local Government (Gashua) a shekarar 1996 har zuwa 2002. Inda malamin ya rike Sakataren Majalisar Malamai na Jihar Yobe na riko na tsawon wata shida.


 Bayan Tafsirin Al-Qur'ani Mai Girma da yake yi a Kofar Halliru, sheikh ya dauki shekaru Goma Sha uku Yana Tafsirin Al-Qur'ani Mai Girma a Masallacin Juma'ah dake kofar Mai martaba sarkin Bade da yamma kafin bisani ya farayin na Dare a Babban Masallacin na fada shine tsawon shekaru.


  Ya Sheikh, ya dawo da makarantar sa zuwa kofar Gidan sa a inda yacigaba da yin Tafsirin Al-Qur'ani Mai Girma tin a shekarar 2011 har izu a bana ta 2022.


   Sheikh Goni Aisami Shine Wanda ya Assasa wa'azin karkara da a keyi a duk karshen wata a kauyikan Gashua, Jakusko, karasuwa, Nguru da Guri a Jihar Jigawa a shekarar 1996 inda muke shiga Kauyika domin karantar da Al'umma sunnar Annabi muhammad (sallallahu Alaihi Wasallam)



  Sheikh Goni munkoyi jajircewa ne akan Aikin Addinin muslunci daga gareshi wajen nuna kauna, kyauta, sakin fuska, Ziyara da jawo mu a Jikin sa sosai domin mu tsaya akan hidimar Addinin muslunci.


 A duk shekara idan shehin malamin zai tafi Aikin Hajj to a inda Yan Agaji suke anan yake sauka Haka ma dawowar sa. Ko a wannan shekara ma ya sheikh a wajen mu ya sauka.


  Sheikh mutun ne Mai son mutane sosai da Gaske Wanda a zahira duk Garin Gashua babu mutum Mai yawan yiwa Al'umma sallama, a duk inda yaga mutum zai daga hannu yayi Masa sallama cikin fara'ah da Annashawa a fuskar sa a koyaushe.


  Sheikh Goni Aisami, mutum ne son a ziyarce shi a Gidan sa domin bayason rabuwa da mutane a kusa da shi. Sheikh Goni malami ne Mai fadin gaskiya akan kowaye komin mulkin sa Kuma komin kudin sa.


 Akwai wani Lokaci da barayi Suka tare mu mundawo daga wajen wa'azi a Garin Dagona, sukayi Mana kaca kaca har sai da muka kwanta a Asibiti Ni da malam. 


  Sheikh Goni malami Mai so da kaunar 'yan Agaji sosai da Gaske a inda duk inda yaga Dan Agaji Yana girmamashi kwarai da Gaske.


  A Ranar rufe Tafsirin sheikh na bana Ina zaune a wajen, sheikh yace Ina kaunar Shehu Abdurrahman Agaji Kamar yadda nake kaunar yayana.


  Shekaran jiya Juma'ah da Daddare wani sojan Nigeria katon Arne ya halaka shi. Ya Allah ka saka Mana.


   Ya Allah ka karbi shahadar Sheikh Muhammad Goni Aisami.


Daga

Shehu A. Abdurrahman Gashua

Comments