Skip to main content

Posts

Showing posts from August, 2022

Tarihin:- Marigayi Sheikh Muhammad Goni Aisami {Ya Sheikh} Gashua

 GWAGWARMAYAR YADA ADDININ MUSLUNCI DA: Marigayi Sheikh Muhammad Goni Aisami {Ya Sheikh} Gashua  A fagen Wa'azi da karantarwar Addinin muslunci akan doron Qur'ani da Sunnah.  Daga: Shehu A. A. Gashua     Shashidi sheikh Muhammad Goni Aisami ya farayin fice ne sosai a fagen Wa'azi da kungiyar Izalah take gudanarwa a mako-mako a Cikin unguwanni dake cikin Garin Gashua a shekarar 1992. Shehin malamin ya iya jawo hankalin Matasa da Dattawa a lokacin da yake wa'azi Kuma cikin shikima da Girmamawa.    Sheikh Goni ya Fara gabatar da Tafsirin Al-Qur'ani Mai Girma a watan Ramadan a Masallacin Juma'ah na kungiyar Jibwis dake unguwar Kofar Halliru Gashua a shekarar 1995 inda Alaramma Idriss Abdurrahman Gashua yake ja Masa Baki.   Ya sheikh ya Zama shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jibwis na Bade Local Government (Gashua) a shekarar 1996 har zuwa 2002. Inda malamin ya rike Sakataren Majalisar Malamai na Jihar Yobe na riko na tsawon wata shida.  Baya...