GWAGWARMAYAR YADA ADDININ MUSLUNCI DA: Marigayi Sheikh Muhammad Goni Aisami {Ya Sheikh} Gashua A fagen Wa'azi da karantarwar Addinin muslunci akan doron Qur'ani da Sunnah. Daga: Shehu A. A. Gashua Shashidi sheikh Muhammad Goni Aisami ya farayin fice ne sosai a fagen Wa'azi da kungiyar Izalah take gudanarwa a mako-mako a Cikin unguwanni dake cikin Garin Gashua a shekarar 1992. Shehin malamin ya iya jawo hankalin Matasa da Dattawa a lokacin da yake wa'azi Kuma cikin shikima da Girmamawa. Sheikh Goni ya Fara gabatar da Tafsirin Al-Qur'ani Mai Girma a watan Ramadan a Masallacin Juma'ah na kungiyar Jibwis dake unguwar Kofar Halliru Gashua a shekarar 1995 inda Alaramma Idriss Abdurrahman Gashua yake ja Masa Baki. Ya sheikh ya Zama shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jibwis na Bade Local Government (Gashua) a shekarar 1996 har zuwa 2002. Inda malamin ya rike Sakataren Majalisar Malamai na Jihar Yobe na riko na tsawon wata shida. Baya...
Tafarkinshiriiya
Tafarkin Shiriya Shafi ne Wanda zai dinga kawo muku abubuwan da suka shafi addini da rayuwar yau da Kullum Kuci gaba da kasancewa damu.